Masu zanga-zangar nuna fushinsu da manufofin gwamnati sun yi arangama da 'yan sanda jiya Asabar a Champs-Elysees da ke birnin Paris, a wani zagaye na zanga-zangar da ake yi ta nuna bijirewa ga Shugaban Faransa Emmanuel Magcron.
WASHINGTON D.C. —
'Yan sanda sun yi ta jefa barkonon tsohuwa da ruwan zafi a shaharren wurin saboda su kori masu zanga-zangar daga ofishoshin Shugaban kasa da ke fadar Elysees Palace.
Dubban mutane ne dai su ka taro a Paris babban biirnin Faransa don yin zanga saboda karin kudin man fetur da aka yi.
Akalla Mutane takwas, ciki har da ‘yan sanda biyu sun rauni a jiya Asabar, a cewar hukumomi.
Tun lokacin da aka fara gudanar da wannan zanga-zangar mako guda da ya gabata, mutum biyu sun rasa rayukansu, lokacin da kusan masu zanga-zangar dubu 250 sanye da riguna masu ruwa dorawa, yawancinsu daga yankunan karkara suka rufe hanyoyi a fadin kasar.