Farfesan ya bude wata makaranta ta koyar da aikin fina-finai sakamakon kalubalen saukar kasuwar fina-finai, game da fasahar da duniya ta ke kai akan fina-finai.
An bude makarantar ta Digital Film and Television Institute ne domin kawar da matsalolin masana'antar Kannywood, inda yake cewa matsalolin da suka danganci kasuwanci fina-finai da cimma yadda duniya ta kai a fina-finai.
Farfesan ya ce dalilin haka ne ya ga ya zama wajibi a koyar da Fim tun daga tushe, kuma a ilmance.
Farfesa Umar Faruk ya ce ita wannan makaranta kafin dalibi ya kammala ta, sai ya hada Fim.
Ya kuma ce makarantar ta dauki tsarin koyar da Fim ne a aikace, wanda wannan ita kadai ce hanyar da za ta koyar da darasin cikin saukin fahimta, inda wannan makaranta ta "Digital Film and Television Institude."
Ya kara cewa abokansu 'yan Kudu masu shirya fina-finai tuni suka yi wa sashen Arewa nisa, dalilin da ya sa a yanzu ake yunkurin bude cibiyoyin da zai koyar da fina-finai.
Ga cikakken rahoton wakiliyar DandalinVOA Baraka Bashir.
Your browser doesn’t support HTML5