Falesdinawa Sun Yi Tofin Allah Tsine Da Rufe Ofishinsu A Washington DC

Ofishin Falesdinawa da aka rufe a nan Washington DC

Amurka ta rufe ofishin Falesdinawa da aka bude shekaru 25 da suka gabata domin ta tilastawa Falesdinawan komawa kan teburin shawarwari da Israila

Litinin gwamnatin shugaba Trump a nan Amurka ta ba da sanarwar rufe ofishin Falasdinawa da ke Washington DC babban Birnin Amurka.

Gwamnatin Amurka ta ce ta dauki matakin ne domin Falesdinawan sun ki su koma kan teburin shawarwari da Israila. Dalili ke nan da Amurka ta ce a rufe ofishin sai ranar da Falesdinawan suka yadda su soma tattaunawa da Israila tare da Amurka a matsayin mai shiga Tsakani. Manufar Amurka ita ce ta tilastawa Falesdinawan su bi umurninta saboda wani kwamiti da Amurkan ta kafa na kirkiro hanyar sasanta bangarorin biyu.

Kafofin labaru kamar jaridar Vanguard ta Nigeria sun ruwaito cewa Amurka ta fusata da Falesdinawa domin yunkurin gurfanar da Israila gaba kotun kasa da kasa da ke binciken manyan laifuka. Falesdinawan sun bukaci kotun ta biniciki Israila akan sake gina wasu matsuguni a a gabar yammacin kogin Jordan da kasha kashen dauki dai dai da Israila ke yi masu.

Saeb Erekat, sakataren kungiyar Falesdinawa y ace” wannan wata manuniya ce ga manufar gwamnatin Trump, ta ladaptar da Falesdinawa tare da katse taimakon kudin da kungiyarsa ke samu domin ayyukan jinkai da suka hada da samar da kiwon lafiya da ilimi” Falesdinawa suna ganin ba komi ba ne illa bita da kulli da Amurka ke yi masu.

Saidai jami’an gwamnatin Amurka sun zargi Falesdinawa da keta ka’idar yarjejeniyar da suka cimma na ci gaba da barin ofishinsu a bude a Birnin Washington.

Idan an tuna shekaru 25 da suka gabata aka sa hannu a Fadar White House a yarjejeniyar da nufin kawo sulhu tsakanin Falesdinawa da Israila.

Husam Zamlot shugaban ofishin Falesdinawa a nan Washington ya fada wa ‘yan jarida a Ramallah cewa “Amurka ta dauki matakin ne domin ta kare Israila daga manyan laifukan da ta aikata kuma ta na ci gaba da aikatawa a yankunan Falesdinawa”.

Falesdinaw sun sha alwashin ci gaba da kokarin gurfanar da Israila a gaba kotun kasa da kasa tare da cewa ba za ta amince da duk wata shawara daga Amurka ba, a saboda yadda Amurka ta amince da Birnin Qudus a matsayin babban Birnin Israila.