WASHINGTON, D.C. —
A karon farko, tawagar ‘yan wasan kungiyar Super Falcons ta Najeriya, ta lashe gasar WAFU bayan da ta lallasa mai masaukin baki, Ivory Coast da ci 5-4 a bugun penarti.
Rahotanni sun ce, gabanin a je bugun daga kai sai mai tsaron gida, bangarorin biyu sun yi kunnen doki da ci 1-1 a filin wasa na Stade Robert Champroux de Macory.
Bayan da aka kwashe mintina 90 sai aka tafi bugun na penarti.
Falcons ta yi nasarar shiga zagayen wasan karshen ne, bayan da ta doke Ghana, wacce ta lashe kofin gasar a bara, ta hanyar bugun penarti a ranar Alhamis.
Ita kuwa Ivory Coast ta doke Mali ne da ci 2-1 a wasan gab da na karshe, inda wannan shi ne karo na biyu da take zuwa wasan karshe ba tare da ta samu nasara ba.