Fafaroma Ya Bayyana Tsananin Damuwa Kan Matakin Trump Game Da Birnin Kudus

Birnin Kudus

Fafaroma ya nuna rashin amincewarsa da shirin da shugaban Amurka Donald Trump keyi na amicewa da Qudus a zaman babban birnin Isra'ila, yayin da sauran kasashen duniya kamar Britaniya suka ce har yanzu Tel Aviv suka sani a zaman hedkwatar Isra'ila.

Yayin da a yau Laraba shugaba Donald Trump ke shirin ayyana cewa Amurka zata amince da birnin kudus a matsayin babban birnin Isra’ila tare da kuma dage ofishin jakadancinta dake Tel Aviv zuwa Kudus, Fafaroma Francis ya nuna “tsananin damuwa” akan wannan matakin, yayinda Turkiyya ta kira taron kungiyar kasashen Musulmi don shata martanin bai-daya da za a maida kan wannan lamarin.

Firayin minista Benjamin Netanyahu bai ambaci batun ba a bayyanarsa gaban jama’a yau Laraba.

Sakataren harkokin wajen Burtaniyya Boris Johnson ya ce kasarsa ba ta da niyyar dage ofishin jakadancin ta daga Tel Aviv.

Kasashen larabawa da na musulmi sun yi gargadin cewa duk wani mataki da Amurka zata dauka na canza inda ofishin jakadancinta yake, zai kara zaman tankiya a yankin tare da gurgunta kokarin Amurka na ganin an cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin larabawa da Isra’ila.