Faduwar Darajar Naira Ya Gurgunta Harkar Fataucin Shanu A Najeriya

Shanun Fulani Makiyaya

Faduwar darajar Naira a kasuwannin duniya ta gurgunta harkar fataken shanu a kasuwar shanu ta kasa da kasa dake garin Mubi, wanda ke kan iyakar Najeriya da makwabtanta na jumhuriyar Kamaru da Nijar.

Kasuwar wadda a baya kimanin motocin tirela 250 zuwa 300 ke lodin shanu zuwa kudancin Najeriya a kowane mako, a halin yanzu tireloli 45 zuwa 50 ne ke lodin shanu daga kasuwar, inji sarkin tiken Mubi Alhaji Rabiu Dan Iya.

Farashin kudin sefa ya tashi da misalin kashi Dari da Hamsin, inda ake canjin jaka Daya na sefa kan Naira 750 kwatankwacin Naira 300 a watannin baya, lamarin da ya yi sanadin karyewar jarin wasu daga cikin fataken, kamar yadda shugaban gamayyar kungiyoyin da ke kasuwar shanu Alhaji Usman Dan Mai Nagge ya yi bayani a hirarsa da muryar Amurka.

Bisa dukkan alamu, faduwar darajar Naira na shafar sauran harkokin kasuwanci a Mubi, garin da ya zama mahadin kasuwanci tsakanin Najeriya da Kamaru da Chadi da kuma musamman sana’ar fata da kudancin Najeriya, inji Shugaba ‘yan kasuwa da masu kananan masana’antu reshen karamar hukumar Mubi, Kwamrad Abdulkadir Musa.

Domin karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Faduwar Darajar Naira Ya Gurgunta Harkar Fataucin Shanu A Najeriya - 2'21"