Fadar White Ta Rufe Wasu Bayanai A Cikin Kasidar Democrat

Shugaba Donald Trump a Fadar White House

Fadar White House ta rufe wasu bayanai da bakar tawada a cikin kasidar da yan Democrati a majalisa suka fitar a kan zargin da bangaren Republican a Majalisar suka yi cewa hukumar FBI tana amfani da ikonta na bicike ta yanda bai dace ba.

Yan Democrat sun fid da kasidar ce a jiya Asabar, makwanni uku bayan da Devin Nunes ya shirya kasidar da ma’aikatan bangare Republican a majalisar wakilai suka tattara.

Fitar da kasidar Democrat ya biyo bayan tattaunawa tsakanin hukumar FBI da babban mamban kwamitin tattara bayanan sirri na Majalisa na Democrat Adam Schiff mai wakiltan jihar California, a kan irin bayanan da yakamata a fitar dasu.

Schiff shine ya rubuta kasidar Democrat a matsayin martanai ga takardan da Nunes ya shirya, dake zargin hukumar FBI da boye wasu bayanai a kan alakar Democrat da da wani bincike mai adawa da takardun da aka yi amfani dasu wurin samun izinin takardan sammaci daga tarayya domin binciken tsohon mai bada shawara ga kwamitin kemfen Trump Carter Page.