Mataimakin sakataren watsa labarai a Fadar House Hogan Gidley, ya shaidawa manema labarai a cikin jirgin sufurin shugaban kasa jiya Litinin cewa, “Babu wata tattaunawa da aka yi, ko hira, game da cire Mr. Mueller”.
Kakakin ya bayyana bacin ran shugaban kasar da binciken da ake gudanarwa kan ko kwamitin yakin neman zaben Trump din yayi wata hulda da bata dace ba da ‘yan kasar Rasha.
“Shugban kasar ya hakikanta cewa, wannan ce bita da kullin siyasa mafi girma a tarihi”, inji Gidley, ya kara jadada abinda shugaba Trump ya wallafa a shafinsa na twitter da safe.
Yadda Trump yake caccakar Mueller a dandalin sada zumunci ya haifar da damuwa cewa, mai yiwuwa shugaban kasar zai cire shi, abinda zai haifar da rudani ga kasar Amurka, ta fuskar tsarin mulki, bisa ga cewar ‘yan majalisa, da masu sharhi kan harkokin sharia, da kuma masana tarihin shugabancin Amurka.