Fadar Shugaban Kasa Ta Wanke Sakataren Gwamntin Tarayya daga Zargin Yin Almundahana

David Lawal Babachir sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya

Wanda yake cikin kwamitin da ya binciki kwangilar yanke ciyawa ta miliyoyin Nera yace sun yi aiki kainda nain kuma wasikar shugaban kasa da ta wanke Lawal Babachir yunkuri ne na neman a birkitar da gaskiya.

Shugaban kwamitin 'yan gudun hijira na majalisar dattawa Sanata Shehu Sani ya maida martani ga wasikar da ta fito daga ofishin Shugaba Buhari dake nuna cewa ba'a yiwa sakataren gwamnatin tarayya Babachir Lawal adalci ba kan batun nome ciyawar kachalla.

Wasikar da shugaban majalisar dattawan ya karanta tace mutane ukku kachal ne cikin tara suka sanya hannu cikin rahoton binciken da ake zargin sakataren gwamnati da yin zarmiya. Kazalika ba'a gayyaci shi sakataren ba ko 'yan kwangilar domin su kare kansu lamarin da ya sa shugaba Buhari ya ki amincewa da bukatar cire David Lawal Babachir daga mukaminsa.

Amma Shehu Sani yace yanada takardar gayyatar sakataren gwamnatin haka kuma wai mutane bakwai ne cikin tara suka sanya hannu akan rahoton. Saboda haka zasu cigaba da fitar da rahoton karshe tare da yi wa fadar shugaban kasa shagube.

Shehu Sani yace a dawo da kudaden da jama'a suka wawure kana a hukumtasu. Yace idan jamai'an gwamnati zasu yi zarmiya a kyalesu ko kuma a karesu yakamata a bude gidajen kurkukun Najeriya duk wani mai laifi ya fita. Rahoto na biyu zai nuna inda aka dinga kwashe kudade tare da asusun da aka sakasu.

Dan majalisar wakilai Ahmed Babba yace yana kokwanton wasikar saboda lamarin ya daure masa kai.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Fadar Shugaban Kasa Ta Wanke Sakataren Gwamntin Tarayya dag Zargin Yin Almundahana 3' 00"