Akan yadda 'yansanda suka kame mutanen biyu Dr. Danlami Alhassan na sashen koyon aikin jarida a Jami'ar Bayero dake Kano yace karan tsaye ne suka yiwa tsarin mulkin kasar.
Matakin da 'yansandan suka dauka ya sabawa ka'idoji da muradun kasar, musamman tafarkin dimokradiya. Inji Dr Alhassan tsarin mulkin kasa ya ba 'yan jarida 'yancin su bayyana abubuwan da gwamnati keyi da bata fito fili ta bayyanawa jama'a ba.
Wani mai sharhi yace dan jarida abokin tafiyar gwamnati ne saboda shi ne mai yada manufofin gwamnati. Yace kame mutanen zai kawowa gwamnati illoli da yawa saboda dan jarida yana da baki. Yace idan wannan gwamnatin na son kanta da arziki to ba dan jarida ba duk wani wanda yake da aikin yi na kasa to ta bishi a hankali.
A cewar wani mai sharhi yanzu yakamata ace yan jarida masu rajin kare hakkin dan Adam da wayewa jama'a kawuna ba'a musguna masu ba. Yace a takaice 'yan jarida su ne fitilar da suka haska al'umma kuma saboda wasu bayyanan da suke yi da basu yiwa gwamnati dadi ba sai ta dauki matakin kamasu ba daidai ba ne. Yace wannan mummunan tabo ne ga gwamnati.
Kungiyar kare hakkin 'yan jarida ta fitar da wata sanarwa da wakilinta Mr. Peter Nganga ya sanyawa hannu. Tace wani shiri ne na sanyawa jaridar Premium Times takunkumi saboda tayi suna akan buga rahotanni dake da nasaba da cin hanci da rashawa da kuma rahotannin dauye hakin bil Adama a Najeriya. Kungiyar ta kira gwamnati da tayi watsi da duk wasu cajin da ake yiwa 'yan jaridar ba tare da bata wani lokaci ba.
Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.