Fadar Shugaba Buhari Zata YI Binciki Cogen da Aka Yiwa Kasafin Kudi

Shugaba Muhammad Buhari

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya sha alwashin binciken cogen da aka yiwa kasafin kudin da ya gabatarwa majalisa

Fadar gwamnatin tarayya da shugaba Buhari ke jagoranta ta yanke shawarar yin bincike akan cogen da aka yiwa kasafin kudin da ya gabatarwa majalisa.

Matsalar badakalar ta dabaibaye harkokin majalisun kasar musamman majalisar wakilai inda ake ganin watakila ma bangaren kakakin da tsohon shugaban kwamitin kasasfin kudi na iya kai juna kotu.

Binciken zai tabo gwamnatocin baya, wato na Obasanjo da Jonathan har da ma ta marigayi Umar YarAdua domin tabbatar cewa wadanda suka aiwatar da irin wannan badakalar a can baya a gurfanar dasu gaban kuliya.

Ministan shari'a Abubakar Malami shi ya bayyana hakan a tattaunawar da ya yi da manema labaru. Yace gudanar da binciken nada mahimmanci domin tabbatar da an kwato dukiyoyin jama'a da wasu na baya suka sata.

Farfasa Mas'ud Ujudud yace gwamnati tana da hurumin binciken badakalar kamar yadda ita majalisar ta yi alkawarin gudanar da bincike da zara ta dawo daga hutu. Gudanar da bincike ai tabbatar da yin adalci.

Ga rahoton Umar Faruk da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Fadar Shugaba Buhari Zata YI Bincike Akan Cogen da Aka Yiwa Kasafin Kudi - 4' 13"