Batun tsige shugaban kasa Goodluck Jonathan tana kasa tana dabu, a majalisar dokokin Najeriya.
Alamu na nuni da cewa akwai rarrabuwan kawuna, akan yanda ake so a gabatar da kudirin a gaban Majalisa, ganin yanda wadansu ke cewa suna da labarin, yukurin tsige Goodluck din wadansu kuma na cewa batun bai kai garesuba.
Alkaluma na nuni da cewa maganan tsige shugaba Goodluck, na kara samun karbuwa, da sa hannun ‘yan majalisu daga jamiyu daban-daban.
Wannan shine karo na farko da ‘yan majalisun wakilai da dattawa, za suyi hadin gwiwa, wajen wukurin tsige shugaban kasa a Najeriya, abun da ya jawon hankalin fadan Gwamnatin tarayya dake Abuja, inda ta fitar da sanarwa na gargadi ga ‘Yan majalisu kan yukurin da suke yi na son tsige shugaban kasa.
Your browser doesn’t support HTML5