Dukkanin malaman addinan kuda biyu sunyi imanin cewa zasu iya bada gagarumar gudunmawa ta yadda za samu nasarar kawar da cin hancin dake kawo cikas wajen samar da ababen ci gaban jama’a.
Mataimaki na musamman ga shugaban kungiyar Kristoci reshen Arewacin Najeriya, Rev Musa Dada, yace cin hanci da rashawa na daya daga cikin abin da Allah baya so, kasancewar hakan yasa suka dage wajen ganin sun wa’azantar, idan kuma wani mutum ya shiga irin wannan hali ba zai yi amfani da hujjar cewa bai sani bane.
Shima Sheik Abdullahi Bala Lau, shugaban kungiyar Izala a Najeriya, yace mayar da hankali wajen bayyanawa talakawa illar cin hancin zai yi tasiri ga shugabanni. Domin idan talakawa suka gane illar cin hancin, duk lokacin da ‘daya daga cikin shugabanni masu yi suka zo neman alfarma ba zasu yi masa ba.
Ko baya ga shugabannin siyasa da ma’aikatan gwamnati akwai matsalar cin hanci da karbar rashawa da tayi katutu a tsakanin ‘yan sanda. Shugaban ‘yan agajin Izala a Najeriya, Injiniya Mustapha Imam, yace suna kokarin fadakar da ‘yan sandan.
Rundunar ‘yan sanda dai ta tashi tsaye wajen yaki da masu bata mata suna ta wannan fuska, a cewar kakakin ‘yan sandan jihar Neja, DSP Bala Elkana, akwai wani bangare rundunar da ake kira CRO, wanda mutane zasu iya kira ko aika sakon karta kwana na rahotan karbar cin hanci domin a hukunta duk wanda aka samu.
A halin yanzu dai kasashen duniya na zurawa gwamnatin shugaba Mohammadu Buhari ido a bangaren yaki da cin hanci da rashawa.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5