Awwal Musa Rafsanjani shugaban kungiyar Cislac da ke fafutukar inganta harkokin majalisun dokoki a Najeriya kana babban wakilin kungiyar kare hakkin dan adam ta Transparency International a kasar ya bayyana matsayarsu akan rashin dacewa da kiran da Ministan sadarwa Najeriya ya yi wa dandalin sada zumunta na facebook da su daina ba da dama ga masu son ta da zaune tsaye da suna fadin albarkacin baki ko neman yanci
Shima ana shi bangaren masanin tsaro a Najeriya Yahuza Ahmad Getso ya ce wadannan kafofi na da nasu muhimmaci ta fuskar tsaro amma yana ganin gazawar gwamnati ne wajen tace na gari da gurbatacce a cikin shafukan da suke yada bayanai ta wannan kafa. Ya na ganin hanawar shiga mulki ne irin na kama karya da hana fadin albarkacin baki
Amma ga masu amfani da wadannan dandalai na sada zumunta ra’ayoyin su sun banbanta da na wadannan masana bisa abubuwan da suke gani yau da kullun.
A hirar shi da Muryar Amurka, Murtala Adamu Jega ya bayyana cewa, idan za’a tsaya ga iya kalaman nuna kiyayya , tunzura jamaa da tada husuma, babu gwamnatin da zata zura ido hakan ya rinka zama mata dan hakki a ido wajen kula da tsaron kasar da ya wajjaba a gareta, ya zaman mata wajibi ta samo hanyar dakile wadannan yan tsirarru da suke jefa rayukan mutane cikin garari ba tare da an takaita yancin fadar baka ba.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5