Everton Ta Daukaka Kara Kan Soke Mata Maki 10 A Gasar Premier

'Yan wasan Everton

Yanzu kungiyar na saman Burnley da banbancin kwallo kuma za ta kara da Nottingham Forest a yau Asabar.

Kungiyar Everton a gasar Premier League ta Ingila ta daukaka kara a wani yunkuri na ganin an dawo mata da makinta 10 da aka soke, saboda ta take ka’idar kudaden da aka kayyadewa kowacce kungiya ta kashe.

Sokewa kungiyar maki 10 shi ne hukunci mafi tsauri da gasar ta Premier League ta taba gani cikin shekaru 31 da aka yi ana gasar.

Hakan ya sa Everton ta fado kasa warwas a teburin gasar har ta shiga rukunin ‘yan dagaji – wato relegation.

Yanzu kungiyar na saman Burnley da banbancin kwallo kuma za ta kara da Nottingham Forest a yau Asabar.

Kungiyar ta Everton na daga cikin mashahuran kungiyoyin da suka ja zarensu a tarihin gasar a baya.