Everton Ta Bukaci Sam Allardyce Ya Zamo Mata Sabon Koci

Kungiyar kwallon kafa ta Everton, dake kasar Ingila, ta ce tana bukatar tsohon mai horas da tawagar ‘yan wasan kasar Ingila, Sam Allardyce, ya zamo mata sabon Koci mai rukon kwarya zuwa karshen kakar wasan bana 2017/18.

Sam Allardyce, mai shekaru 63 da haihuwa zai maye gurbin tsohon kocin Everton ne Ronald Koeman, wanda kungiyar ta sallama bayan Arsenal ta lallasa ta daci 5-2 a gidan Evarton, a gasar Firimiyar bana.

Kungiyar tana bukatar Sam Allardyce, yayi aiki tare da tsohon kocin Leicester city Craig Shakespeare, mai shekaru 54 a duniya, a matsayin mataimakin sa.

Har ila yau Everton ta ce zata rika biyansa kudi fam dubu dari £100, a matsayin albashi duk sati.

Kungiyar ta Everton, ta ce tana son su zo su fitar da kulob dinne daga halin da ya ke ciki.

Everton, dai ta yi wasanni goma sha daya a gasar Firimiya lig na kasar Ingila na shekarar 2017/18, kuma ta samu nasara a wasanni uku kacal, ta yi kunnen doki biyu, an doketa a wasanni shida sa’an nan tana da maki 11, haka kuma tana matsayi na goma sha biyar daga kasan tebur.

Daga karshe idan hakan ya tabbata Sam Allardyce zai fara wasansa na farko a kungiyar da tsohon kulob dinsa Crystal palace.

Your browser doesn’t support HTML5

Everton Ta Bukaci Sam Allardyce Ya Zamo Mata Sabon Koci