EURO 2024: Wasannin Kusa Da Na Karshe

'Yan wasan Faransa suna atisaye

A ranar Lahadi 14 ga watan Yuli za a buga wasan karshe a filin wasa na Olympiastadion da ke birnin Berlin.

An kammala shirye-shiryen karawar da za a yi zagayen kusa da na karshe a gasar cin kofin nahiyar turai na Euro 2024 da ake yi a Jamus.

Kasar Sifaniya da ta yi waje rod da Jamus mai masaukin baki da ci 2-1 za ta kara da Faransa, wacce ita kuma ta yi waje da tawagar su Ronaldo ta Portugal da ci 5-3 a bugun fenariti.

Kazalika Netherlands wacce ta fitar da Turkiya da ci 2-1 za ta hadu da Ingila wacce ta doke Switzerland da ci 5-3 a bugun fenariti.

'Yan wasan Sifaniya (Hoto: Kirill KUDRYAVTSEV / AFP)

Wasan Sifaniya da Faransa zai wakana ne a filin wasa na Munich Arena da ke birnin na Munich a Jamus a ranar Talata.

Wasan Netherlands da Ingila kuma za a kara ne a filin wasa na BVB Dortmund da ke birnin na Dortmond a ranar Laraba.

A ranar Lahadi 14 ga watan Yuli za a buga wasan karshe a filin wasa na Olympiastadion da ke birnin Berlin.