EURO 2024: Magoya Bayan Turkiyya Na Murnar Kai Wa Kwata-Fainal

EURO-2024-AUT da TUR

Turkiyya ta yi nasara a wasanta da Austria a zagayen ‘yan 16 na gasar cin kofin nahiyar Turai ta EURO 2024 a ranar Talata, lamarin da ya janyo barkewar murna ga ‘yan Turkiyya da ke zaune a kasashen duniya.

Meril Demiral ne ya zura wa Turkiyya kwallaye biyu a wasan da suka yi nasara da ci 2-1 da ya bai wa magoya bayan Turkiyya kwarin gwiwa za su taka rawa a gasar EURO 2024, bayan da suka yi rashin nasara da ci 3-2 a wasan kusa da na karshe a 2008.

Kasar Holland ta yi nasara da 3-0 a kan Romania a wasan da suka buga a ranar Talata, inda za su buga wasan kwata-fainal a ranar 6 ga watan Yuli a Berlin.

Kwallaye biyu da Demiral ya zura sun zo ne daga kwana biyu da Arda Guler ya dauko.

Magoya bayan Austria sun yin ta jefo kwalabe da kofuna kan dan wasan tsakiyar Real Madrid mai shekaru 19 a lokacin da yake shirin dauko kwana ta biyu, sannan bayan da Demiral ya zura kwallo ta biyu, Guler ya kalli magoya bayan Austria kuma ya sanya yatsan sa daya yana nuna kunnansa.

Turkiyya dai ta buga wasan ba tare da kyaftin din ta ba Hakan Calhanoglu da aka dakatar, inda rashin tsoron da Guler ya nuna wajen taka kwallo ya ba da mamaki.

Arda Gular na daya daga cikin taurarin matasa masu hazaka a Turai kuma shi ne dan wasan Turkiyya na farko da ya lashe kofin zakarun Turai a kakar wasan da ta gabata.

Ya yi bajinta sosai a wasan inda ya kusa zura kwallo bayan da ya buga kwallo daga tazarar mita 50 yayin da mai tsaron raga na Austria Patrick Pentz ya ke nesa da ragarshi.