An tabbatar da jadawalin zagayen daf dana kusa da na karshe na gasar kasashen Turai ta “Euro 2024”.
Mafi daukar hankali a jadawalin shine karawar Jamus da Sifaniya data Faransa da Portugal.
An hada tawagar Ingila da kasar Switzerland.
Da kyar tawagar ta Ingila ta kwaci kanta daga hannun kasar Slovakia a gasar, sakamakon farke ci daya mai ban haushi da Jude Bellingham yayi a minti na 96 da take wasa, kafin daga bisani Harry Kane ya kara daya wacce ta bada nasara ana cikin karin lokaci.
Cristiano Ronaldo da tawagarsa sun samu gurbi a zagayen daf dana karshen inda zasu hadu da kasar Faransa, bayan da suka yi galaba akan Slovenia a bugun fenariti a yayin da tawagar da tawagar Faransan, ta kai zagayen na kwatafainal ba tare da wani daga cikin ‘yan wasanta ya zura kwallo a raga ba bayan data samu nasara akan kasar Belgium da ci 1 da nema sakamakon cin gida da wani dan wasan Belgium yayi a karshen karawar.
Tawagar Sifaniya tayi matukar kayatarwa a nasarar data samu akan kasar Georgia da 4 da nema duk da an ci ta kwallo 1 a farkon wasan, a yayin da ita kuma Jamus tayi waje da kasar Denmark daga gasar.
Ga cikakken jadawalin yadda zagayen kwatafainal din zai kasance, ciki harda lokacin take wasa:
Ranar Juma’a, 5 ga watan Yuli
Sifaniya da Jamus - a filin wasa na Stuttgart da karfe 5 na yamma
Portugal da Faransa -a filin wasa na Volksparkstadion dake Hamburg da karfe 8 na dare
Ranar Asabar, 6 ga watan Yuli
Ingila da Switzerland-filin wasa na Merkur Spiel Arena dake Dusseldorf da karfe 5 na yamma
Netherlands da Turkiya- a filin wasa na Olympiastadion dake Berlin da karfe 8 na dare