ETHIOPIA: An Cafke Mutane 30 Akan Bam da Ya Tashi a Wurin Gangamin Siyasa a Addis Ababa

Gangamin goyon bayan Firai Ministan Habaha Abiy Ahmed,

Shugaban 'Yan sandan kasar Habasha ko Ethiopia, Zeinu Jemal ya sanar da cafke mutane 30 dangane da tashin bam a wani gangamin siyasa da ya yi sanadin mutuwar mutane biyu

An cafke mutum 30 da ake zargi na da hannu a wata fashewa da ta auku a wani gangamin siyasa a Addis Ababa, wacce ta yi sanadin mutuwar mutum biyu a cewar kafar yada labarai mallakar gwamnatin Habasha, wacce ta ruwaito labarin daga wasu majiyoyin ‘yan sanda.

Adadin wadanda ake zargi da hannu a wannan hari da aka kai da gurneti, ya haura mutum shida da aka kama a baya.

Yayin wata hira da ya yi da kafar yada labarai ta gwamnatin Habasha, shugaban ma’aikatar ‘yan sandan tarayya, Zeinu Jemal, ya ce “adadin wadanda ake zargi a harin wanda aka kai a wani wuri da ake kira Meskel Square ya kai 30, amma ba tare da ya yi cikakken bayani.

Jami’ai sun ce mutum 150 suka jikkata a fashewar, yayin da ma’aikatar lafiya ta ba da tabbacin karin mutuwar mutum na biyu a jiya Lahadi.