Shugaban kwamitin amintattu na gamayyar kungiyoyin Arewacin Najeriya, Alh. Nastura Ashir Sharif wanda ke jawabi a taron manema labaru a Kaduna ya ce lokacin da ya kamata gwamnati ta dauki mataki kan zanga-zangar ya yi.
Ganin yadda zanga-zangar ta jirkice zuwa kone-kone da kashe-kashe dai ya sa wasu neman gwamnati ta saka karfi don dakatar da ita, duk da cewa mafi akasarin ‘yan kasa da kuma masu sa ido a kasashen ketare sun ce amfani da karfin soja kan masu zanga zangar bai dace ba. A gefe daya kuma, kwararru a fannin harkokin shari’a na kira da a bi matakan da doka ta shinfida domin shawo kan wannan lamari ba tare da an kuntata ko kuma take hakin ‘yan kasa ba.
an-fafata-tsakanin-masu-zanga-zangar-endsars-da-yan-kasuwa-a-jos
zanga-zanga-majalisar-tarayya-na-bukatar-buhari-ya-bayyana-matakansa
amurka-muna-kallon-cin-zarafin-da-akewa-masu-zanga-zanga-a-najeriya
A hirar sa da Muryar Amurka lauya mai-zaman kanshi a Kaduna, Barr. El-zubair Abubakar ya bayyana cewa, kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba kowanne dan kasa ‘yancin yin zanga zanga ko da kuwa shi kadai ne, amma ta lumana ba tare da tada hankali ko kuma ta’adi ba.
Lauyan ya bayyana cewa, bisa ga dokar kasa, mutum zai iya gudanar da zanga zanga ba tare da tada hankali ko fitina, ko kuntatawa wani, ko kuma tada hankali wani ba, amma idan akasin haka ya faru, ya zama ke nan wanda ya yi haka ya keta doka, saboda haka hukumomi su kuma suna da hakkin kare doka ta wajen daukar matakin da doka ta tanada na kawo karshen tashin hankalin.
Tun a yammacin Litinin dai gamayyar kungiyoyin Arewacin Najeriya ta sanar da dakatar da zanga-zangar da ta fara yayin zuwa yanzu wasu jihohin Najeriya da dama su ka saka dokar hana zirga-zirga domin kawo karshen zanga-zangar da ta rikide ta koma tashin hankali.
Saurari cikakken rahoton Isah Lawal Ikara cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5