#EndSARS: Kungiyar Amnesty Ta Zargi Hukumomin Najeriya Da Rufa-Rufa

Zanga Zangar #ENDSARS.

Kungiyar kare hakkokin bil’adama ta kasa da kasa Amnesty International ta yi kira ga hukumomin Najeriya su daina rufa-rufa kan batun kisan gillan da aka yi wa masu zanga a gadar Lekki.

A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na internet, Kungiyar ta bayyana cewa hotona da kuma bidiyo da aka dauka a lokacin da lamarin ya faru ,sun nuna a fili lokacin da motocin sojoji suka bar sansanin Bonny dake tafiyar kimanin minti bakwai daga Lekki, da misalin karfe 6.29 na yamma ranar 20 ga watan Oktoba.

Kungiyar ta ce an kuma nuna hotunan motocin a inda lamarin ya faru da misalin karfe 6.45 na yamma,daidai lokacin da ake zarginsu da bude wuta kan masu zanga zangar lumana da ke neman ganin bayan rundunar ‘yan sanda mai yaki da ‘yan fashi da makami SARS, sabili da yadda rundunar ta yi kaurin suna wajen gasawa al’umma akuba.

Darektan kungiyar kare hakin bil’adama ta Amnesty a Najeriya Osai Ojigho ya bayyana cewa, “abinda ya faru a Lekki ya bi salon hukumin Najeriya na yin rufa-rufa duk lokacin da jami’an tsaron kasar suka yi wa mutane kisan gilla.”

Darektan ya kara da cewa, “bayan mako guda da aukuwar lamarin, Najeriya ba ta amsa muhimman tambayoyi ba. Misali, wanene ya bada umarnin budewa masu zanga zangar lumana wuta? Menene ya sa aka cire na’urorin daukar hotunan bidiyo da ke wurin kafin aukuwar lamarin? Kuma menene ya sa aka dauke wutar lantarki a wurin ‘yan mintoci kafin sojoji su budewa masu zanga- zanga wuta?”

Masu Zanga-Zangar Sai An Soke Rundunar SARS a Abuja

Yace banda musun cewa sojoji ne suka budewa masu zanga zangar wuta, har wa yau hukumi sun musanta adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon harin da sojoji suka kai wa masu zanga-zanga“

Kungiyar Amnesty International ta sake yin kira ga hukumomin Najeriya su hukunta wadanda suke da hanu a budewa masu zanga-zangar lumanar wuta, ta kuma kare wadanda suke taruka kamar yadda dokar kasa ta basu ‘yancin gudanarwa.

endsars-matasan-najeriya-sun-fadi-dalilinsu-na-zanga-zanga

endsars-batutuwa-16-a-jawabin-shugaba-buhari

endsars-matasan-arewa-sun-bukaci-gwamnati-ta-kawo-karshen-zanga-zanga

Kungiyar ta rika sa ido tare da kula da yadda lamura ke gudana a duk fadin Najeriya tun da aka fara zanga-zangar #EndSars ranar 8 ga watan Oktoba. Ta kuma bayyana cewa a kalla mutane 56 suka mutu tun da aka fara zanga-zangar a kasar. .

Zanga Zangar #ENDSARS

Matasa sun jagoranci zanga-zangar lunama a titunan birane da dama suna neman a kawo karshen gasawa jama’a aya a hannu da rundunar ‘yan sanda mai yaki da ‘yan fashi da makami SARS ke aikatawa.