Kungiyar mabiya mazhabar Shi'a ta almajiran Malam Ibrahim El-Zakzaky IMN, ta ce ta sulhunta takaddamar duba malamin, biyo bayan sakon sauti da yake nuna fargabar barazana ga rayuwarsa a asibitin kasar India.
Sakon na sauti ne, wanda IMN ta ce hakika Malam El-Zakzaky ne, kuma ta na sane da yayata shi, na bayyana bukatar El-Zakzaky na dawowa Najeriya domin canza wurin neman magani, zuwa Malaysia ko Turkiyya.
Matsayin kungiyar IMN a yanzu ta bakin kakakinta Ibrahim Musa, an shawo kan lamarin, domin da ma ya taso ne don rashin ganin asalin likitocin da aka yi magana da su karkashin wata kungiyar kare hakkin 'yan Adama a London.
Yanzu dai za a zura a ga jinyar El-Zakzaky da uwargidan sa Zeentu a asibitin na Medanta da ke New Delhi, babban kasar ta India.
A cikakken rahoton daga wakilin Muryar Amurka Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5