Almajiran shugaban ‘yan Shia na Najeriya Ibrahim El-Zazzaky sun ce ba su san inda a ka kai jagaoran su ba bayan saukar sa a filin saukar jirage na Nnamdi Azikwe da ke Abuja.
Mai magana da yawun kungiyar IMN ta 'yan Shi'a a Nigeria, Muhammad Ibrahim Gamawa, ya baiyana cewa almajirran sun taru a flin jirgin saman Abuja domin tarar El-Zazzaky amma sai a ka fita da shi ta wata hanya, sannan aka tafi inda ba su sani ba.
Yanzu dai kungiyar ta El-Zazzaky ta IMN, a takaice, ta ce za ta binciki inda a ka kai malamin kafin sanin matakin gaba da zasu dauka.
Gabannin dawowar sa, El-Zazzaky ya ce an nemi cusa ma sa likitocin da bai yarda da su ba a Indiya, shi ya sa ya zabi dawowa Najeriya, don neman tafiya a wasu kasashen, kamar Indonesia, da Malaysia ko Turkiyya.
Gwamnatin Najeriya ta zargi El-Zazzaky da yunkurin neman sullube doka, a yayin da ya fita ketare, don har ma ya nemi amshe Fasfo din sa.
Ga cikakken rahoton daga wakilin Muryar Amurka Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5