El - Zakzaky Ba Zai Gudu Ba - Kakakin 'Yan Shi'a

Muhammad Ibrahim Gamawa

A hirar shi da wakilin Muryar Amurka, Muhammad Ibrahim Gamawa, wanda shine kakakin 'yan Shia ta IMN a Abuja, yace sun tabbatar da cewa ko an bar Zakzaky ya je India domin neman magani, ba zai gudu ba.

Malam Gamawa, kakakin almajiran El-Zakzaky, yace ba ta yadda za a yi El-Zakzaky ya gudu, ko neman mafakar siyasa a Indiya in ya tafi asibiti a birnin New Delhi.

Gamawa, a bayanin sa kan sharudan da gwamnatin Kaduna ta Nasir El-Rufa'i ta gindaya kan fitar Zakzaky, ya ce shata sharudan alamu ne na damuwar hukuma..

Gamawa ya ce lauyan kungiyar ta El-Zakzaky, Femi Falana, na kwatanta sharudan a matsayin marasa tasiri.

Ga cikakken rahoton hirar daga wakilin Muryar Amurka, Nasiru Adamu El-Hikaya.

Your browser doesn’t support HTML5

El - Zakzaky Ba Zai Gudu Ba - Kakakin 'Yan Shi'a