El Rufai Ya Kori Daukacin Ma’aitakan Jinya Da Suka Shiga Yajin Aiki

Ma'iakatan jinya a bakin aiki (Photo de Guillem Sartorio / AFP)

“An ba ma’aikatar lafiya umurnin ta tallata mukamin ma’aikatan jinyar domin a dauki wasu sabbi ba tare da bata lokaci ba, don su maye gurbin wadanda aka kora.”

Rahotanni daga jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin jihar na cewa, Gwamna Malam Nasiru El Rufai ya ba da umurnin a kori daukacin ma’aikatan jinyar jihar da ke kasa da mataki na 14.

Matakin na zuwa ne bayan da ma’aikatan jinyar suka shiga yajin aikin da aka fara a jihar a ranar Litinin, don nuna adawa da sallamar abokanan aikinsu sama da dubu bakwai da gwamnati ta yi.

Mai magana da yawun Gwamna El Rufai, Muyiwa Adekeye ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.

“Ma’aikatar lafiya za ta kori dukkan ma’aikatan jinya da ke kasa da mataki na 14 saboda sun shiga yajin aiki haramtacce.” Adekeye ya ce.

Ya kara da cewa, “an ba ma’aikatar lafiya umurnin ta tallata mukamin ma’aikatan jinyar domin a dauki wasu sabbi ba tare da bata lokaci ba, don su maye gurbin wadanda aka kora.”

Daukan wannan mataki har ila yau na zuwa ne bayan da gwamnatin jihar ta Kaduna ta zargi wasu ma’aikatan jinya da cire na’urar numfashin wani jariri dan wata biyu a lokacin da suka shiga yajin aikin.

Sanarwar Adekeye ta ce an dauki sunayen ma’aikatan jinyar su uku da ke aiki a asibitin horarwa na Barau Dikko kuma za su fuskanci tuhuma kan “yunkurin yin kisa.”

Ita dai gwamnatin jihar ta Kaduna ta ayyana yajin aikin a matsayin haramtacce, domin a cewarta, ya kassara harkokin yau da kullum a jihar ta Kaduna.

Tun bayan farawar yajin aikin, an rufe bankuna, asibitoci da filin tashin jirage a jihar an kuma ga dogayen layukan shan mai.

Da safiyar ranar Talata, gwamnatin jihar ta ayyana shugaban kungiyar kwadago ta NLC ta kasa Ayuba Wabba a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo.

Gwamna El Rufai yana zargin Wabba da wasu shugabannin kungiyar wadanda suka shiga zanga-zanga a jihar da yunkurin kassara tattalin arzikin jihar.

Wasu rahotanni sun ce wasu matasa sun far wa masu zanga-zangar da makamai a ranar Talata.