Kawo yanzu bincike ake cigaba da yi akan badakalar sayen makaman yaki da ya sa hukumar sojojin Najeriya ta mika wasu hafsoshinta guda goma sha biyu domin a bincikesu.
An gano badakalar ne a ofishin tsohon mai ba shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro Kanar Sambo Dasuki mai ritaya inda ake zargin an yi sama da fadi da wuri na gugan wuri na dalar Amurka miliyan dubu biyu da miliyan dari daya.
Shi dai Sambo Dasuki tun awan gaba da aka yi masa daga gidansa a watan Disambar bara yake zaman wakafi. Ya samu beli amma jami'an tsaron kaya wato DSS suka cigaba da yin garkuwa dashi bisa ga dalilan sabbin zargi. Amma lauyansa ya sake shigar da karar belinsa wadda za'a saurara ranar uku ga watan gobe.
Sambo Dasuki ya hakikance da cewa duk kudaden da ya karbo ya kuma kashe da izinin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ne batun da tuni shi tsohon shugaban kasar ya musanta.
Akan rashin gayyatar Goodluck Jonathan a ji ta bakinsa ita EFCC tace har yanzu tana kan bincike ne.
Da 'yan jarida suka yiwa Solomon Dalung tambaya akankin kama Jonathan sai yace bincike bai kai kansa ba tukunna. Idan ya kai za'a gayyaceshi. Yace mutane su tuna lokacin da bincike ya kai kan wani aminin shugaban kasa Buhari an kamashi kuma ya biya kudin. Saboda haka idan har na hannun daman Buhari bai tsira ba to ko Jonathan ba zai tsira ba muddin bincike ya nuna yana da hannu cikin badakalar.
Su ma 'yan majalisa sunce kada ariga malam masallaci. A bari sai an gama bincike.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5