Hukumar EFCC mai yaki da almundahana a Najeriya ta sanar da yin gagarumin kamen mutane 792 saboda aikata laifuffuka dake da nasaba da zambar zuba jarin kudin kirifto da ta soyayyar bogi.
Daraktan yada labaran EFCC, Wilson Uwujaren, wanda ya yi wa manema labarai jawabi a harabar ofishin hukumar dake Legas a yau Litinin yace an kama mutanen ne a Talatar data gabata 10 ga Disamban da muke ciki, a wani samamen ba zata da aka kai maboyarsu, a wani bene mai hawa 7 da ake kira da ginin Big Leaf, mai lamba 7, kan titin Oyin Jolayemi, a tsibirin Victoria, dake jihar Legas.
Uwujarem ya kara da cewa “nasarar ta biyo bayan bayanan sirrin da aka samu da watannin da suka shafe suna tattara bayanai da sanya idanu akan al’amuran gungun. Bakin hauren da aka kama sun hada da ‘yan China 148 da ‘yan kasar Philipines 40 da ‘yan Kazastan 2 da dan Pakistan 1 da kuma dan Indonesia guda,”.
A cewarsa, an sanya na’urorin komfutar zamani a dukkanin hawan benen, inda a bene na 5 kawai masu bincike sun kano layukan waya 500 na kamfanonin wayar Najeriya daban-daban da aka saya domin aikata laifi.