Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC, ta gurfanar da Khareem Oluwaseyi gaban kotu, tana zarginsa da yin amfani da sunan shugaban ma’aikatar Shari’ar Amurka Jeff Session, yana aikawa mutane sakon email da zummar danfara.
Sai dai Oluwaseyi, ya musanta zargin da ake masa lokacin da EFCC ta gurfanar da shi gaban wata kotu a jihar Lagos, tana mai tuhumarsa da aikata laifuka biyar. Lauyan EFCC, Mista A.M Ocholi ya gabatarwa da kutu shedu dake tabbatar da cewa wanda ake tuhumar ya aikata laifukan a ranar 29 ga watan Yunin wannan shekarar.
Wanda ake zargin dai ya bude akwatunan email kamar haka; jeffsessions54@gmail.com da compbellellaine390@gmail.com, inda yake amfani da su wajen aikawa da wasiku na neman kudi daga jama’a, da sunan zai taimaka musu ko samar musu da wata alfarma.
Yanzu dai Alkalin kotun, Oyindamola Ogala, ya bayar da umarnin ci gaba da ajiye wanda ake tuhumar a gidan yari, har sai ranar 10 ga watan Satumba, domin sauraron bukatar bada beli idan ya cika sharudan kutu.
Ayyukan ‘yan danfara ta kafofin sadarwar zamani na daya daga cikin muhimman ayyukan hukumar EFCC. Sai dai rahotanni na nuni da cewa ana ci gaba da samun karuwar ‘yan danfarar a Najeriya.
Domin cikakken bayani saurari rahotan Babangida Jibrin.
Your browser doesn’t support HTML5