Kungiyar ECOWAS ta tura Shugaban Jamhuriyar Benin Patrice Talon zuwa Nijar kan yunkurin juyin mulkin da aka yi a kasar, kamar yadda gidan talbijin na kasa na NTA ya sanar a Najeriya.
Wannan mataki ya biyo bayan ziyarar da Shugaba Talon ya kai wa Tinubu a fadarsa da ke Abuja a ranar Laraba.
Da safiyar ranar Laraba wasu dakarun da ke tsaorn fadar shugban kasar Jamhuriyar Nijar suka yi wani abu mai kama da yunkurin juyin mulki, lamarin da ake ganin bai yi nasara ba.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton babu cikakken bayani kana bin da ke faruwa a fadar shugaban kasar wacce ke Yamai.
Gabanin tura Talon, kungiyar ta ECOWAS ta ce ba za ta lamunci juyi mulki a Nijar ba, tana mai Allah wadai da matakin da dakarun suka dauka.
““Ya kamata dukkan masu ruwa da tsaki a Jamhuriyar Nijar su fahimci cewa, shugabancin kungiyar ECOWAS da sauran masu muradun kare tsarin mulkin dimokradiyya a sassan duniya, ba za su lamunci duk wani abu da zai gurgunta tsarin mulkin dimokradiyya da aka kafa na zababbiyar gwamnati a kasar ba.” Tinubu ya ce cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.
Bayanai sun yi nuni da cewa Shugaba Bazoum Mohamed na tsare a hannun dakarun da suka yi yunkurin juyin mulkin, amma babu wani abu da ya shafi lafiyarsa.