ECOWAS Ta Tanadi Dakarun Da Za Su Kawar Da Jammeh

Shugaban Gambia Yahya Jammeh a taron ECOWAS a Abuja, Disamba 16, 2015.

Kungiyar ECOWAS ko kuma CEDEAO ta bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika, ta yi barazanar yin amfani da karfin tuwo wajen kawar da gwamnatin shugaba Yahya Jammeh na Gambia, muddin ya ki sauka daga kan mulki idan wa’adinsa ya kare a watan Gobe.

Shugaban kungiyar ta ECOWAS ko kuma CEDEAO, Marcel Alain de Souza, ya gayawa manema labarai a jiya Juma’a cewa, an tanadi dakaru na musamman wadanda su ke cikin shirin ko-ta- kwana.

Ya kuma kara da cewa an zabi kasar Senegal a matsayin wacce za ta jagoranci kawar da gwamnatin ta Jammeh, domin ita ce kasa da ke kewaye da Gambia ta bangarori uku.

Koda yake a baya kasar ta Senegal ta ce daukar matakin soji shi zai kasance zabi na karshe a yunkurin da ake yi na kokarin shawo kan rikicin siyasar kasar na Gambia.

A ranar 18 ga watan Janairun shekarar 2017 wa'adin shugaba Jammeh zai kawo karshe.

Shugaba Jammeh wanda ya mulki Gambia na tsawon shekaru 22, a baya ya amince da shan kayi a zaben da aka yi a watan Disamba, amma daga baya sai ya fake da cewa an tafka magudi a zaben.