ECOWAS Ta Shirya Taron Fadakar Da Kawuna Kan Hada-hadar Kudi

Mahalarta Taron Kudi Na Ecowas A Lagos

Kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yanmacin Afirka, ECOWAS, ta shirya wani taron karawa juna sani ga jami’an bankuna da cibiyoyin hada-hadar kudi da inshora akan hanyoyin kaucewa anfani da kudaden da aka haramta wajen hada hadar makamai ko muggan kwayoyi a yankin dama duniya baki daya.

Taron na kwanaki uku yana samun wakilci daga bangarorin hada-hadar kudi da kasuwanci dama tsaro daga babban bankin Nigeria da kuma sauran bangarorin hana safara da halatta kudaden haramun cikin dukiyar kasa.

Malam Idris Isa Buhari babban jami,ine a babban bankin Nigeria ya yi karin haske game da wannan taro,inda ya ce idan an lura yanzu a Nigeria batun ta’addanci da cin hanci da rashawa sun yi katutu, don haka akwai bukatar tashi tsaye domin magance wannan matsalar kafin ta fi karfin hukumomi, kuma da zara ba’a tashi ba wannan ayyuka na ta’aadanci za su iya kai kasar su baro.

Sauda yawa dai bankuna na taimakawa masu hallatta kudaden haramun wajen ajiye masu kudaden, ko yaya bankuna ke ji game da wannan zargi?

Alhaji Bilyaminu Inuwa Yakasai, wakili ne daga bankin Jaiz, ya ce a gaskiya babu dokar da ta hana bankuna karban kudade daga mutanen da kawai ake zargi da kudaden haramun ne, sai dai abinda bankuna ke yi domin taimakawa wajen kame irin wadannan masu safarar shine sanarwa hukumomin tsaro domin daukan mataki.

Wannan dai ba shine karon farko ba da cibiyar ke shirya tarukan bita a kan hada-hadan kudaden ba, sai dai Timothy Melaye ya ce taron na da mahinmanci wajen saninan makaman aiki ga ma’aikatan banki da sauran yan kasuwa akan hanyoyin da za’a bi domin magance safara ko hada-hadar kudaden haramun a tsakanin kasashen yammacin Afirka dama duniya baki daya ta anfani da bankuna da sauran cibiyoyin kudi na duniya.

Kowa ya sani yan taa'dd da kudi suke anfani dashi don haka a duk lokacin da babu kudi Kaman kifi suke a ruwa idan ya rasa ruwa yam utu inji Melaye. Kokarin su shine mu hana fataucin makamai da sauran ayyukan ta’addanci da safaran makamai ko kwayoyi ta hanyoyin yin anfani da kudi daban daban.

A saurari rahoton Banagida Jibrin

Your browser doesn’t support HTML5

ECOWAS Ta Shirya Taron Fadakar Da Kawuna Kan Haha hadar Kudi - 3' 59"