ECOWAS Na Ci Gaba Da Kokarin Ceto Kasar Mali

Shugaba Buhari Da Mahamadou Issoufou, jiga jigan kungiyar ECOWAS

Masu ruwa da tsaki na ci gaba da kokarin inganta al'amura a kasar Mali tun bayan da aka yi juyin mulki. Na baya bayan nan shi ne kokarin kawar da takunkumi a kasar ta Mali.

Jagororin wata tawaga da ke wakiltar kungiyar kasahen Afirka ta Yamma, suna fatan cewa za a dage takumkumin da aka kakaba wa kasar Mali bayan rantsar da shugaban kasar rikon kwarya da aka yi a ranar Jumma’a, wata daya bayan juyin mulkin da sojoji suka yi.

Tsohon Shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan, wanda shi ne manzo na musamman na kasashe 15 na kungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta Yamma (ECOWAS), ya yaba wa shugabannin juyin mulkin a lokacin da ya kai ziyara Mali a jiya Laraba.

Shugabannin ECOWAS a taronsu a Abuja, Disamba 16, 2015.

Jonathan ya fada wa manema labarai cewa, sojojin, wadanda suka karbi mulki suna yin aiki daidai da abin da shugabannin ECOWAS suke so.

Sannan ya ce Mali ba ta bukatar takunkumi wadanda ba su da amfani ga yankin da kuma sauran duniya.