WASHINGTON D.C. —
Sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya yi kira ga wadanda su ka yi alkawarin taimakawa a yakin da ake yi da cutar Ebola da su cika alkawuransu.
Guterres ya yi wanan kiran ne yayin da ya kai ziyara Congo don bayar da goyon bayansa ga yakin da ake yi da cutar.
Ya gaya ma menama labarai a birnin Kinshasa jiya Litinin cewa Majalisar Dinki Duniya ta samu kashi 15% ne kadai na abin da ta ke bukata don yakar annobar Ebola a ragowar tsawon shekarar, kafin ya je wata ganawa da Shugaba, Felix Tshisekedi, na Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.
Shugaban na Majalisar Dinkin Duniya ya ce duk ci gaba da jinkiri wajen samun kudi daga masu taimakawa zai zama kenan “mun gaza a yaki da Ebolar.”