Ebola Ta Kashe Wata Mata A Laberiya

A Laberiya wata mace ta mutu, a Guinea kuma an yiwa mutane 800 allurar rigakafin kamuwa da cutar Ebola, yayinda rahotanni suke nuni d a cewa ana ci gaba da samun sabbin mutane da suka kamu da cutar, duk da cewa hukumomi sun ayyana kasashen a zaman wadanda su shawo kan cutar a farkon wannan shekara.

Hukumar kiwon lafiya ta duniya ta fada yau jumma'a cewa, matar da ta mutun, ana kan hanyar kaita asibiti ne a Monrovia babban birnin kasar, lokacin da rai yayi halinsa.
Hukumar kiwon lafiya ta duniyar, tare hukumomin kasar nan da nan suka tura tawagar masana zuwa ga yankin da matar ta fito a fitar birnin na Monrovia, da kuma cibiyar lafiya da ake mata jinya da farko. Tuni aka fara bincike, kuma ana neman a gano dukkan mutane da suka yi mu'amala da ita.