“Ziyarar ta kunshi fitowa karara mu fada musu cewa matakin da suka dauka zai shafi alakarmu da taimakon da muke ba su ta fuskar tattalin arziki, wanda ba mu da zabi illa mu janye su bisa tsarin doka, idan har ba a maido da tsarin dimokradiyya ba.” In ji Nuland.
Washington D.C. —
Shirin Duniyar Amurka na wannan mako zai duba ziyarar da Mukaddashiyar Mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka Victori Nuland ta kai Jamhuriyar Nijar, a yunkurin da Amurka ke yi na ganin ta shawo kan rikicin shugabancin da ya biyo juyin mulki da sojoji suka yi.
Your browser doesn’t support HTML5