DUNIYAR AMURKA: Takaddama Kan Fadada Damar Karbar Karin Bashi Da Gwamnatin Biden Take So Ta Yi, Mayu 12, 2023

Mahmud Lalo

Sakatariyar Baitul Malin Amurka, Janet Yellen, ta yi gargadin cewa idan har ba a fadada damar karbar bashin ba, nan da farkon watan Yuni gwamnati za ta rasa kudaden da za ta kashe.

Shugaban Amurka Joe Biden na kokarin kwantarwa da kasuwannin hada-hadar kudade hankali, yayin da ya rage makonni kasar ta shiga kangin gaza samun kudaden da za ta gudanar da harkokinta na yau da kullum a karon farko a tarihin kasar, saboda fadar shugaban kasa da majalisar dokokin sun gaza cimma matsaya kan fadada Kofar ciyo karin bashi.

Saurari cikakken shirin cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

DUNIYAR AMURKA: Takaddama Kan Fadada Damar Karbar Karin Bashi Da Gwamnatin Biden Take So Ta Yi - 6'00". mp3