DUNIYAR AMURKA: Makomar Daliban Ukraine Da Ke Karatu A Amurka - 04 Maris, 2022

Mahmud Lalo

Bisa alkaluma da ma’aikatar kidayar jama'a ta Amurka ta fitar, akwai akalla ‘yan kasar Ukraine dubu 105 da ke zaune a Amurka, wadanda ba 'yan kasa ba, 2,000 daga cikinsu, dalibai ne da ka iya cin gajiyar shirin na samar a kariya na TPS.

Amurka ta bi sahun kawayenta wajen kakabawa Shugaban Rasha Vladimir Putin da manyan jami’an gwamnatinsa takunkumi, saboda yakin da suke yi a Ukraine yayin masu rajin ganin an dabbaka ayyukan agaji ke kira ga gwamnatin Amurka ta agazawa ‘yan Ukraine da ke zaune a nan Amurka musamman dalibai da ke karatu.

Yau batun da shirin Duniyar Amurka na wannan mako zai yi nazari akai kenan, tare da Mahmud Lalo.

Your browser doesn’t support HTML5

DUNIYAR AMURKA: Makomar Daliban Ukraine Da Ke Karatu A Amurka - 6'26"