Yawancin wadanda suke kai harin kunar bakin wake 'yan nan wurin ne amma an kamasu ne karfi da yaj an canza masu kwakwalwa domin su aikata duk abunda aka sasu su yi.
Inji Jakada Hassan Muhammad a yi misali da 'yan matan Chibok da suka ce su ba zasu koma wurin iyayensu ba, kuma sun yi hakan ne domin an juya musu hankali.Irin wadanan matsalolin kasashen duniya sun fahimci abun da kasar ke ciki dangane da Boko Haram
Dangane da cewa wasu na bada 'ya'yansu su yi kunar bakin wake, Jakadan yace babu wanda zai ba da 'yarsa ko dansa domin ya yi kunar bakin wake. Yana mai cewa Boko Haram sun kashe shugabannin gargajiya da masu unguwa da dai sauran shugabannin wuraren da suka mamaye da can. Wadanda suka tsira kaman a Bama da kafa suka isa Maiduguri, irinsu ba zasu ba da 'ya'yansu ba.
Akan cewa rashin Buhari ya sa aka samu karin hare hare daga Boko Haram, sai Jakadan yace ba haka ba ne. Yana ganin bayan nasarorin da suka samu sun dan huta ne shi ya sa 'yan Boko Haram suka fara afka masu.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5