Duniya Na Dab Da Fuskantar Barazanar Na'urori Masu Kwakwalwa

Wata kungiya dake fafutukar neman sauya matsayar ci gaba da sarrafa munanan mutum-mutuman na’urorin masu sarrafa kawunan su wadanda za a iya amfani da su domin harba makami kuma ya fada dai-dai inda ake bukata sun koka da babbar murya.

Gamayyar kungiyoyi masu zaman kansu guda 65 wadanda suke wanna kamfe sun yi kira da babbar murya musamman akan yadda lokaci ke kurewa domin hana ci gaba da inganta wannan fasaha domin a cewar su duniya da dab da shiga wani lakaci kokuma yanayi da wannan fasaha ka iya zama barana ga duniya baki daya.

Wanda ya jagoranci kungiyar Mr Richard Moyes, ya yi gargadin cewa duniya ba dab da shiga wani mawuyacin lokaci da na’urori masu kwakwalwa zasu maye gurbin dan a’adam.

Daga karshe kungiyar kare hakkin bil’adama ta human right watch, wadan da suka kirkiro wannan kamfe, sun bayyana cewa cikin munanan mutum-mutuman makaman da duniya ta dade da mallaka sun hada da jirgi mara matuki.