Murtala Joda, matashin dan siyasa ya ce abinda ke jefa matasa ga harkar bangar siyasa, bai wuce yadda iyaye 'yan siyasa ke amfani da matasa daidai lokacin yakin zaben domin cimma manufofinsu, maimako a koya masu siyasa tun daga tushe.
Sai dai ayi amfani da su domin cin zabe da zarar sun cimma nasara sai a manta da matasan, wanda hakan ya jefa matasa a matsayin 'yan koren siyasa da basu da amfani sai a lokacin yakin zabe.
Joda ya ce lokaci yayi da matasa zasu farga su kuma san wanda ya dace su zaba, tare da cewar an haifar wa matasa talauci da rashin aikin yi ta hanyar kashe masu zuciya da mayar da su 'yan banga da karfin tsiya.
A yanzu kuwa dole matashi ya tashi ya kwatarwa kansa yanci, domin huce takaicin barin matasa a baya da ake yi a harkar demokradiya.
Ya ce suna kokarin jawo ra’ayin wasu matasan da suke ganin zasu kai kasar nan ga ci gaba, tare da tabbatar da an dama da matasa domin su fito a wasu madafan iko domin fitar da su daga kunya da bangar siyasa da matsala ta shaye-shaye da ke ciwa jama'a tuwo a kwarya.
Your browser doesn’t support HTML5