Duk Da Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Sudan Ta Kudu Ana Zaman 'Dar 'Dar

Shugaban Sudan Ta Kudu Salva Kiir ya yi kira ga abokin jayyarsa Riek Machar da su gana, a wani yinkuri na ceto yarjajjeniyar zaman lafiyar da aka cimma, wacce ke fuskantar barazana sanadiyyar barin wutar bindigogi da atilare na kwana da kwanaki a Juba, baban birnin kasar.

Mazuna birnin na Juba sun gaya ma Muryar Amurka cewa zuwa jiya Alhamis an samu kwanciyar hankali, kwanaki uku bayan da yarjajjeniyar saman lafiyar ta fara aiki, to amma mutane na cigaba da zama cikin firgita kuma ba su tura 'ya'yansu makaranta saboda don kar yakin ya sake barkewa ya rutsa da su.

Da ya ke magana da manema labarai a Fadar Shugaban kasa da ke Juba, Shugaba Kiir ya ce shi bai son a cigaba da zubar da jini a Sudan Ta Kudu don haka ya na so Machar, Mataimakin Shugaban kasar na Daya, ya dawo don su shata mafita.

Machar ya daina fita bainar jama'a tun bayan da aka yi taron manema labarai na ran 8 ga watan Yuli da shi, a daidai lokacin da sojojin gwamnati da na 'yan tawayen ke fafatawa a wajen Fadar da sauran sassan birnin na Juba.