Mutumin da 'yansandan suka kama sai ya kwace bindigar wani dansanda ya kashe jami'an 'yansandan guda hudu kana ya yi garkuwa da wasu fursinoni.
'Yansanda sun killace ginin dake Kapenguria kuma suna kokarin kawo karshen wannan ta'asa domin su kubutar da firsinonin da ake garkuwa dasu inji ta bakin babban jami'in 'yansandan Kenya Joseph Boinnet..
Boinnet yace mutumin ya yi kokarin arcewa bayan da ya kashe jami'ansu, amma 'yansandan da suka isa ginin sun dakile duk wani kokarin da ya yi .
Mutumin da ya aikata wannan aika-aikar ana kyautata zaton shi ne yake samar wa kungiyar al-Shabab mai alaka da kungiyar al-Qaida, kurata. Kungiyar tana da cibiyarta ne a kasar Somalia.
Al-Shabab ita ce take da alhakin kai hare-hare a Kenya cikin 'yan shekarun nan abun da tace mayarda martani ne kan take taken sojojin Keyan dake fafatawa da kungiyar a Somalia.
Tun farko yau Alhamis Bonnet yace 'yan kungiyar al-Shabab sun yi kokarin kai hari a wani caji ofis na 'yansandan dake yankin tekun kasar amma basu ci nasara ba.
Boinnet yace 'yansandan sun jajirce kuma sun fafata da 'yan ta'adan kuma sun kashe da yawa cikinsu amma bai bada adadin 'yan al-Shabab din da suka kashe ba.