Hukumar zaben kasar Kamaru ta lashi takobin cewar za ta gudanar da zaben shugaban kasa a duk fadin kasar, har da bangaren 'yan awaren kasar masu anfani da harshen Ingilishi.
Alhaji Abdulkadir dan asalin garin Baminda kuma yana cikin masu fada a ji a kungiyar 'yan awaren, ya yi shakkar gudanar da zabe a yankin su. Ya ce da wuya a yi zabe a wurin su saboda mutane fiye da dubu 50 na gudun hijira a Nigeria. Wasu kuma sama da dubu 400 sun bazama ko sun rikide cikin wasu al'ummomi, baicin wadanda suke hannu sojoji da 'yan sanda. Ya ce a yankin kullum ana harbe harbe abun da ya hana masu tsayawa takara zuwa yankin yin kemfen.
A cewar Alhaji Abdulkadir, gwamnantin kasar ba ta dauki wani mataki mai kyau ba. Ya ce an roki gwamnati ta janye sojoji ta tattauna da mutanen amma ta ki, maimakon hakan ma kullum kara sojoji ta keyi.Sojojin kuma ba lafiya su ke kawowa mutanen ba. Ya ce gwamnati ta sake mutanen da ta kama. Wadanda suka fice daga kasar ta yi masu ahuwa su dawo.
Shi ko shugaban bangaren kula da jama'a na hukumar zabe Alhaji Zakari Muhammadu, ya dage za'a yi zabe a duk fadin kasar. Ya ce sun shirya tsaf kuma an baza jami'an tsaro. Ya ce aikinsu ne su gudanar da zaben. Akan tsaro ya ce gwamnatin Kamaru ta dauki matakan yin hakan.
A saurari rahoton Muhammad Awal Garba
Your browser doesn’t support HTML5