Sanata Dansadau wanda ya yi majalisar dattawa daga 1999 zuwa 2007 yace ko noma ma ba’a iya yi musamman a karamar hukumar Maru saboda wai, akwai sakaci daga matakin jihar.
Yace idan kasa ta zama haka ana iya kafa dokar ta baci, a dakatar da gwamna har sai lokacin da alamura suka daidaita, dalili ke nan da ya rubutawa shugaban kasa.
Akan dalilin da ya sa bai zanta da gwamnan jihar ta Zamfara ba sai yace ya zauna dashi, ya bashi shawarwari amma yaki dauka. Ko wannan ganin ma sai da ya yi wata kafin ya iya ganinsa.
Da yake mayarda martini sakataren jam’’iyyar APC na jihar Zamfara Alhaji Sani Gwamna yace bukatar ta Dansadau bata ma taso ba.
Yace duk maganganun Sanatan babu daya da yake da gaskiya ciki. Yace lamarin tsaro ya shafi gwamnatin tarayya kuma duk wanda yake jihar ya san irin matakin da gwamnatin tarayya ta dauka da ma sauran makwaftan jihohi game da barayin shanun. Shi ma gwamnan yana nashi kokarin har ma yana ganawa da sarakuna da shugabannin kananan hukumomi da jami’an tsaro.
Gwamnatin tarayya ta tura sojoji da ‘yansanda da sauran jami’an tsaro zuwa jihar ta Zamfara.
Sojojin Najeriya suna cigaba da kakkabe barayin shanu inda ta kashe uku har ma ta gano wasu babura da dama da makamai da sauran kayan aikinsu.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5