Dubban masu zanga-zanga sun hallara a birnin Washington da sauran birane a fadin Amurka da ma duniya baki daya jiya Asabar, su na masu Allah wadai da banbancin launin fata da kuma amfani da karfi fiye da kima da ‘yan sanda ke yi, makwanni kusan biyu bayan mutuwar wani ba- Amurke bakar fata a hannun ‘yan sanda.
A biranen fadin Amurka an barke da zanga-zangar bukatar a rika adalci, a daina nuna banbancin jinsi a sha’anin shari’a da kuma yadda ‘yan sanda ke gudanar da ayyukansu, kuma an cigaba da wannan zanga-zangar ce kulluyaumin tun bayan mutuwar George Floyd ranar 25 ga watan Mayu a birnin Minneapolis na jahar Minnesota, bayan da wani dan sanda mai suna Derek Chauvin ya sa gwiwarsa ya danne wuyar Floyd na tsawon minti 9, yayin da Floyd ya yi ta rokonsa cewa bai iya numfashi. Wannan ne dai na baya bayan nan a jerin mace-mace da bakaken fata kan yi a hannun ‘yan sanda.
(Magajiyar Garin Washington, Muriel Bowser na tattaki da masu zanga-zanga)
Jim kadan bayan nan, a zanga-zangar da aka yi ta yi a birane a fadin duniya, mutane na tsararraki daban daban da jinsuna daban daban a fadin duniya sun yi ta daga murya su na cewa, “Ba na iya numfashi,” kalaman da marigayi Floyd ya yi amfani da su a karshen rayuwarsa.
A Washington, babban birnin Amurka, masu zanga-zangar lumana sun yi maci cikin zafin rana da kuma rashin iska da yamma a unguwanni da dama, da kuma wajejen ginin Majalisar Dokokin Tarayyar Amurka da ma tsawon dandalin kasa na National Mall.
Magajiyar Birnin Washington, Muriel Bowser, ta yi jawabi ga taron jama’a da yammacin jiya a babbar hanyar nan da jiya aka sa mata suna ‘Black Lives Matter Plaza” wato shirayin gwagwarmayar ‘yanto ‘yancin bakake, wadda ke arewa da wurin shakatawar nan na Lafayette Park da fadar White House. Ranar Jumma’a Magajiyar Gari Bowser ta sa wani mai aikin zane zane ya rubuta kalmar “Black Lives Matter,” wato ‘Rayukan Bakake Na Da Muhimmanci’ da manyan haruffa a kan titin 16th Street Northwest.