Dubban mutane ne suka tarbi tawagar ‘yan wasan Argentina a Buenos Aires babban birnin kasar a ranar Talata a lokacin da ta sauka bayan lashe kofin duniya.
Argentina ta doke Faransa da ci 4-2 a wasan karshe da bugun fenariti bayan da bangarorin biyu suka tashi da ci 3-3.
Mutane sun yi cincirundo don su kyalla ido kan kofin gasar ta duniya wanda ‘yan wasan na Argentina suka zagaya da shi birnin, yayin da suke kan wata mota kirar bas mai budadden kai.
Wannan nasara da tawagar ‘yan wasan ta Argentina ta samu karkashin jagorancin Lionel Messi, na zuwa ne a daidai lokacin da matsin tattalin arziki ya addabi jama’a, nasarar da ake ganin ta zo a daidai lokacin da ake bukata, duba da cewa za ta sanyaya zukatan jama’a.