Hukumar kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, ta dubban mutane sun rasa matsuguni a kasar Chadi a sanadin ambaliyar ruwan da ta biyo bayan ruwan sama mafi yawa da kasar ta gani cikin shekaru 40.
Kakakin hukumar, Adrian Edwards, ya shaidawa VOA jumma'a cewa wannan ambaliya ta shafi dukkan sassan kasar.
Ya ce a wani gari ma dake arewacin kasar, iyalai dubu daya da dari takwas ne suka rasa gidajensu.
Amma ya ce har yanzu ba a san iyakacin barnar da wannan ambaliya ta haifar ba. Ya shaidawa VOA cewa ana fuskantar wuya wajen samun bayani saboda yankunan dake cikin lungu wadanda a da ma akwai wuyar kaiwa gare su, balle kuma ga shi ambaliyar ta toshe hanyar kaiwagare su.
Ruwan sama kamar da bakin kwarya da ake yi a kasar Chadi ya biyo bayan fari na shekaru biyu. A yayin da wasu suka yi fatar cewa ruwan zai taimaka musu wajen samun amfanin gona mai yawa, mutane da yawa sun wayi gari gonakinsu sun kasance karkashin ruwa mai yawa da ya kwanta, yayin da shuke-shukensu suka lalace.
Wasu 'yan Chadi da suka yi hasarar gidajensu a sanadin ambaliyar sun koma su na zama da abokai ko a makarantu. Wasu kuwa sun rasa matsugunin da zai kare su daga ruwan saman da ake ci gaba da yi.