Dubban mutane su na gudu daga manyan alkaryu na kasar Pakistan a yayin da ruwan ambaliya mai dan karen yawa ya doshi kudancin kasar.
Rundunar sojojin Pakistan tana taimakawa wajen kwashe mutane daga lardin Punjab a tsakiyar kasar da kuma lardin Sindh na kudanci, inda ake sa ran za a ci gaba da ganin ruwan damina kamar da bakin kwarya.
Tuni ruwan da yayi ambaliyar ya ragargaza yankin arewa maso yammacin kasar, inda ya bar mutane fiye da miliyan uku ba su da gidajen kwana ko amfanin gonar da suka shuka, sannan ba su da abinci ko ruwan sha mai kyau.
Mutane akalla dubu daya da dari biyar suka mutu a wannan ambaliya.
Jami'ai sun ce wasu mutanen su akalla 20 sun mutu yau alhamis a lokacin da wata motar safa ta fada cikin wani kogin da ya batse da ruwa a yankin Kashmir dake hannun Pakistan.
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon, ya tura wakilinsa na musamman Jean-Maurice Ripert, zuwa Pakistan domin dafa wa tawagar majalisar dake kasar tana aikin agazawa wadanda suka tagayyara a sanadin ambaliyar.
Shugabannin Pakistan su na kara fuskantar fushin 'yan kasa saboda abinda ake gani a zaman jan kafar da gwamnati ta yi kafin ta fara agazawa. Wasu da dama sun bayyana bacin rai da shawarar shugaba Asif Ali Zardari ta ci gaba da yin ziyara a Turai a yayin da kasar ke fuskantar wannan bala'i na ambaliya.