Dan uwan Salihu, Abdullahi Tanko Yakasai ne ya sanar da sakin nasa a shafinsa na Twitter.
“Alhamdulillahi, an saki dan uwana @dawisu. Muna godiya ga kowa da kowa.” Abdullahi ya rubuta.
A karshen makon da ya gabata hukumar ta DSS ta kama Yakasai bayan wasu wallafe-wallafe da ya yi a shafin Twitter yana sukar lamirin gwamnatin shugaba Buhari kan yadda al’amuran tsaro ke tabarbarewa a kasar.
“Idan gwamnati ba za ta iya ba ta yi murabus,” Yakasai ya rubuta a shafinsa na Twitter.
Ya kuma kara da cewa jam’iyyar APC ta gaza a kowanne mataki na kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Amma tuni ya riga ya goge rubutun daga shafin nasa.
Da farko hukumar ta DSS ta musanta cewa tana tsare da Salihu, wanda aka fi sani da “@dawisu” a shafin Twitter, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce kan ‘yancin fadin albarkacin baki.
Amma daga baya hukumar ta DSS ta fito ta amsa cewa tana tsare da shi.
Cikin wata sanarwa da kakakinta Peter Afunanya ya fitar, hukumar ta ce tana binciken Yakasai ne ba don rubutun da ya yi ba.
“Ana bincikensa ne kan wasu al’amura ba don ya ra’ayin da ya bayyana ba a shafin sada zumunta kamar yadda wasu suke zargi.” Afunanya ya ce.
Rahotanni sun ce a lokacin ana tsare da shi, gwamnatin jihar Kano ta kore shi daga bakin aikinsa, kamar yadda wata sanarwa da kwamishinan yada labarai Muhammed Garba ta nuna.
Wannan ba shi ne karon farko da Yakasai yake sukar gwamnatinsu ta APC ba, wacce ita ke mulki a Kano karkashin gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
A watan Oktoban shekarar da ta gabata ya taba sukar Buhari kan zanga zangar Endsars da ta mamaye wasu sassan kasar lamarin da ya sa har aka dakatar da shi daga aiki amma daga baya aka mayar da shi.